Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya zama Shugaban jam’iyar APC ta Kasa

Published

on

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC a Najeriya ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.

An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Ranar 17 ga watan Yuli ne dai Shugaban jam’iyar na ƙasar sanata Abdullahi Adamu da babban sakaraten jam’iyyar Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu na shugabancin jam’iyar.

Inda jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

To sai dai a ranar 27 ga watan Yuli ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanya sunan Sanata Abubakar Kyari cikin jerin sunayen da ya aika Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!