Labaran Kano
Ganduje yayi Allah wadai da masu sace mutane
Gwamnatin Kano ta maida martani kan sace ‘yan jihar Kano da aka yi, tana mai yabawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da sauran hukumomin tsaro saboda namijin kokarin da yayi wajen kwato yara tara da ak yi zargin sace su anan Kano aka kuma sayar da su a jihar Anambra.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da sakataren yada labaran sa Abba Anwar ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ce hakan wata ‘yarmanuniya ce ga kishin kasa da kuma hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro da suka hada da rundunar ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da da sojoji wajen tabbatar da an kama bata garin.
Ta cikin sanarwar, Ganduje ya ce hukumomin tsaron sun yi amfani da kayayyakin zamani wajen ceto yaran, da kuma yaki da fashi da makami a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Rubutu masu alaka:
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Adamawa
Yadda ‘Yansandan Kano suka cafke wadanda suka kone magidanci
Rudunar ‘yan sanda ta Puffer Adder gami da ta yaki da sace mutane da yin garkuwa da su sun kama wani mutum mai suna Paul Owne mai shekaru 37 da Mercy Paul da take da shekaru 38 da Emmanuel Igwe mai shekaru 34 da Ebere Ogbodo mai shekaru 45 da Louis Duru mai shekaru 30 da kuma Monica Oracha mai shekaru 50 na kokarin daukar daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da shi Haruna Bako zuwa jihar Anambra.
A cewar rundunar an ceto sauran mutum 8 ne a hannun wadanda suka siye su a jihar Anambra.