Labarai
Ganduje zai rarraba takunkumin rufe baki da hanci miliyan 2 ga Kanawa
Gwamnatin jihar Kano ta ce, zata raba takunkumin rufe baki da hanci miliyan 2 a dukkanin masarautu 5 da ke jihar nan, don kare jama’a daga kamuwa da cutar Korona.
Mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan a ya yin da gwamnatin Kano ta ke ganawa da sarakunan jihar Kano 5 tare da wasu malaman jihar Kano bayan da aka sake samun bullar cutar Korona karu na biyu.
Gwamnan Kano ya kara da cewar, gwamnatin sa ta gana da sarakunan gargajiya da kuma wasu daga cikin malamai a jihar Kano ne kasancewar sun fi kusa da jama’a, adon haka ya buakace su da su wayar da kan mutane yadda zasu Kare kansu daga wannan Annobar Corona.
D ayake jawabi Mataimakin babban jami’in kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar na jihar Kano Dakta Sabitu Shu’aibu Shanono ya ce biyo bayan sake bullar cutar COVID-19 a sassan duniya a karo na biyu, jihar Kano ta bayyana cewar mutane goma sha bakwai ne suka rasa rayukan su ta sanadiyar cutar tun daga watan Disambar bara zuwa Janairu, 2021,
Dakta Sabitu Shuaibu Shanono ne ya bayyana hakan a ya yin da Gwamnan Kano ke ganawa da sarakuna guda biyar da hakimai dangane da sake dawowar cutar Karo na biyu.
Shugaban kwamitin kar ta kwanan na Kano ya ce, daga watan Nuwamba 2020 zuwa Janairu, 2021, jihar Kano ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar har 827 tun bayan da Annobar ta biyu ta zo don haka ya yi kira ga Sarkunan don wayar da kan jama’a kan yadda za su Kare kansu.
Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa masu rike da masarautun gargajiya da wasu manyan malaman Kano da kososhin gwamnatin Kano ne suka halacci ganawar.
You must be logged in to post a comment Login