Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai rarraba takunkumin rufe baki da hanci miliyan 2 ga Kanawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce,   zata raba takunkumin rufe baki da hanci  miliyan 2 a dukkanin masarautu 5 da ke jihar nan, don kare jama’a daga kamuwa da cutar Korona.

Mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan  a ya yin da gwamnatin Kano ta ke ganawa da sarakunan jihar Kano 5 tare da wasu malaman jihar Kano bayan da aka sake samun bullar cutar Korona karu na biyu.

Gwamnan Kano ya kara da cewar,  gwamnatin sa  ta gana da  sarakunan gargajiya da kuma wasu daga cikin malamai a jihar  Kano ne kasancewar sun fi kusa da jama’a, adon haka ya buakace su da su wayar da kan mutane yadda zasu Kare kansu daga wannan Annobar Corona.

D ayake jawabi Mataimakin babban jami’in kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar na jihar Kano Dakta Sabitu Shu’aibu  Shanono ya ce biyo bayan sake bullar cutar COVID-19 a sassan duniya a  karo na biyu, jihar Kano ta bayyana cewar mutane goma sha bakwai ne suka rasa rayukan su ta sanadiyar cutar tun daga watan Disambar bara  zuwa Janairu, 2021,

Dakta Sabitu Shuaibu Shanono ne ya bayyana hakan a ya yin da Gwamnan Kano ke ganawa da sarakuna guda biyar da hakimai dangane da sake dawowar cutar Karo na biyu.

Shugaban kwamitin kar ta kwanan na Kano ya ce, daga watan Nuwamba 2020 zuwa Janairu, 2021, jihar  Kano ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar har 827 tun bayan da Annobar ta biyu ta zo don haka ya yi kira ga Sarkunan don wayar da kan jama’a kan yadda za su Kare kansu.

Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano  Zahrau Nasir ta ruwaito cewa masu rike da masarautun gargajiya da wasu manyan malaman Kano da kososhin gwamnatin Kano ne suka halacci ganawar.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!