Kaduna
Mahaifin Malam Albaniy Zaria ya rasu
Mahaifin malamin nan Malam Albani Zariya ya rasu.
Mahaifin na sa mai suna Malam Adam Ɗanjuma ya rasu da asubahin ranar Laraba.
Ministan sadarwa na kasa Isah Ali Pantami wanda aminin marigayi Albanin Zariyan ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.
Anyi jana’izar marigayin da safiyar Laraba, a gidansa da ke unguwar Muchiya a garin Zaria.
Kisan Malam Albaniy Zaria
A watan Fabrairu na shekarar 2014 ne wasu ƴan bindiga suka hallaka Malam Albani Zariya tare da matarsa da ɗansa.
Ƴan bindigar sun buɗe wa malamin da iyalansa wuta a kan hanyarsa ta komawa gida daga makaranta.
Nan take matarsa ta rasu, inda shi kuma da ɗan na sa aka garzaya da su asibitin Wusasa da ke Zariya.
A nan kuma Allah ya karɓi rayukansu.
You must be logged in to post a comment Login