Addini
Garkuwa da mutane: mahaifin daya daga cikin daliban da ‘yan bindiga su ka sace a Kaduna, ya rasu
Mahaifin daya daga cikin dalibai da ‘yan bindiga su ka sace a Kaduna ya rasu sanadiyar bugun zuciya.
Mahaifin daya daga cikin dalibai 39 ‘yan kwalejin nazarin tsirrai da gandun daji ta kasa da ke Kaduna, wadanda ‘yan bindiga suka sace su ka yi garkuwa da su, mai suna Ibrahim Shamaki, ya rasu.
Ibrahim Shamaki shine mahaifin Fatima Shamak, daya daga cikin daliban wanda ta sanya hijabi da aka nunosu cikin faifan bidiyo da ‘yan bikdigar suka saki a kafafen sada zumunta.
Wata majiya ta shaidawa gidan talabijin na Channels cewa, marigayi Ibrahim Shamaki, ya rasu ne sakamakon ciwon zuciya wanda ya gamu dashi jim kadan bayan samun labarin sace ‘yarsa da ‘yan bindiga su ka yi.
A cewar majiyar ya rasu ne da yammacin yau Juma’a lokacin da iyalansa ke kokarin kaishi asibiti don duba lafiyarsa bayan da jikin yayi tsanani.
Mutuwar ta sa na zuwa ne awanni kadan bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta gudanar da wani taro da iyayen daliban da ‘yan bindigar su ka sace.
You must be logged in to post a comment Login