Labarai
Gazawar gwamnati ne rashin samarwa al’umma ruwa – Farfesa Kamilu Fagge
Masanin siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, gazawar gwamnati ne rashin samarwa da al’ummar ta ruwan sha.
A cewar masanin batun ruwa da titina na gaba-gaba cikin abubuwan da ƴan siyasar Najeriya ke yin yaƙin neman zaɓe da su.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na bayyana hakan, yayin da yake yin fashin baƙi kan batun da gwamnati ta yi na cewar ba za ta iya wadatar da jihar Kano da ruwan sha ba.
“Batun ruwa da titina da sauran ababan more rayuwa a cikin gari, haƙƙine da ya shafi gwamnati, matuƙar ta gaza samar da su, ya nuna ci bayan da ake samu a siyasar Najeriya”.
“Hakan yana nuna gwamnati tafi bawa wani bangaren muhimmanci, duk da cewa ruwa da shi ake rayuwa, ba wai yin gada ko titi ba” a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge.
Ya ci gaba da cewa, “Ana yin gwamnati ne don jama’a, don haka samar da tsaro, harkokin lafiya, ruwan sha, abinci sune abubuwan da ya kamata su zo a gaba, ba wai wasu abubuwa da ba su shafi al’ummar ba kai tsaye”.
A ranar Talatar da ta gaba ne hukumar bada ruwan sha ta jihar Kano ta ce, zai yi wahala a samar da ruwan sha a kowanne lungu da saƙo na jihar Kano, ko da kuwa za’a yi amfani da dukkan kuɗaɗen Kano.
You must be logged in to post a comment Login