Labarai
Gazawar shugabannin da suka gabata ne matsalar Najeria – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC Peter Obi, ya ce matsalar kasar nan, ba ta ta’allaka ne kadai kan karancin albarkatu ba, sai dai gazawar shugabannin da suka gabata wajen amfani da albarkatun ƙasar yadda ya kamata.
Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan halin da Najeriya ke ciki, inda ya ce kasar na da albarkatun da za su iya kawo ci gaba da inganta rayuwar al’umma.
Ya ce duk da wadatar albarkatun kasa da na dan Adam, kasar na ci gaba da fuskantar matsalolin talauci, rashin aikin yi da sauran kalubalen tattalin arziki.
Peter Obi ya ce akwai bukatar shugabanci mai daukar alhaki da kuma amfani da dukiyar kasa domin amfanin jama’a.
You must be logged in to post a comment Login