Labarai
Gwamnatin tarayya ta yi martani kan masu sukar jawabin shugaban kasa

Mai baiwa shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya mayar da martani ga wasu ’yan siyasa da suka soki jawabin shugaban kasa na ranar ’yancin kai.
Onanuga ya ce wasu daga cikin ’yan siyasar sun riga sun shirya martaninsu tun kafin Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabin ranar 1 ga Oktoba.
A wani sako da ya wallafa a ranar Juma’a, Onanuga ya ce masu sukar jawabin sun yi watsi da bayanan da shugaban kasar ya yi kan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin sa ke aiwatarwa.
Ya kuma bayyana cewa bai dace a yi suka ba tare da la’akari da abin da shugaban kasar ya bayyana kan manufofin tattalin arziki ba.
You must be logged in to post a comment Login