Labarai
IBP ta ƙulla yarjejeniya da Ma’aikatar Lafiya ta Kano kan bibiyar kashe kuɗaɗe

Cibiyar International Budget Partnership (IBP) ta ƙulla yarjejeniya da Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, tare da samar da manhajar da za ta bayyana yadda ma’aikatar da sauran hukumomin kiwon lafiya ke kashe kuɗaɗen da aka ware musu.
Da yake jawabi bayan sanya hannu kan yarjejeniyar a Kano, shugaban cibiyar ta IBP a Najeriya, Dakta Olayinka Babalola, wanda shugaban sashen gudanar da tsare-tsare na cibiyar, Onyekachi Chuano, ya wakilta, ya ce tsarin zai bunƙasa harkokin kiwon lafiya tare da sauƙaƙa hanyoyin bibiyar kashe kuɗaɗen.
Shi kuwa jami’in da ke wakiltar gidauniyar Gates Foundation a Kano, Dakta Shamsuddin Skan, ya ce manhajar za ta taimaka wa gwamnati da manyan jami’an ma’aikatun kiwon lafiya wajen samun bayanai kan yadda ake kashe kuɗaɗe a ma’aikatun cikin sauƙi ta wayoyin hannu.
Da yake nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce ma’aikatar da gwamnatin jihar za su ci gaba da aiki tare da cibiyar, bisa la’akari da muhimmancin manhajar da ta samar wajen inganta harkokin kiwon lafiya.
Taron sanya hannu kan yarjejeniyar ya samu halartar hukumomin kiwon lafiya na jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a fannin, inda aka jaddada muhimmancin inganta sa ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen kiwon lafiya.
You must be logged in to post a comment Login