Connect with us

Labarai

Gina majalisar dattawan jami’ar Bayero babbar nasara ce – FARFESA

Published

on

Shugaban Jami’ar Bayero da ke nan Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya bayyana cewa daya daga cikin nasarori da ya samu a yayin mulkin sa shi ne kammala ginin sabuwar majalisar dattawan jami’ar a makaranatar, da kuma fito da dabarun ci gaban ilimi tare da inganta shi.

Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka Da Hantsi na nan tashar freedom redio

Shugaban Jami’ar mai barin gado, ya ce kammala ginin majalisar dattawan jami’ar wanda zai taimakawa makarantar wajen gudanar da taro kasancewar sauran dakunan sun yiwa jami’ar kadan.

A nasa bangaren Alhaji Usman yahya kamsila wanda shine mamallakin kamfanin da yayi gini sabuwar majalisar, ya bayyana cewar babban nasara ce ga kasar nan, na ganin an dogara da kamfanonin gida wajan gudanar da gine-gine kamar yadda suka samar da wannan gini.

Ya kuma ce, amfani da kayyayakin gini da aka sarrafa a Najeriya da kuma amfani da ma’aikata yan asalin kasar zai kara taimakawa wajan habaka tattalin arziki a fadin kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!