Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Gwajin Korona: An dage dawowa gasar kwallon kafa ta mata a Najeriya

Published

on

An dage dawowa ci gaba da wasannin rana ta biyar a gasar kwallon kafa ta mata a Najeriya sakamakon rashin cika ka’idojin gwajin cutar Korona a tsakanin kungiyoyin dake buga gasar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa dasa hannun babban jami’in dake kula da shirya gasar Faith Ben-Anuge ya fitar game da ranar dawowa ci gaba da gasar.

A baya dai an tsaida ranar goma sha daya ga watan Janairu domin dawowa fagen gasar kafin daga bisani a dage zuwa ranar goma sha uku ga watan na Janairu.

Ben-Anuge, ya ce, an baiwa kowace kungiya wa’adin mako guda don gudanar da gwajin cutar Korona ga ‘yan wasa da kuma ma’aikanta tare da tura sakamakon gwajin ga hukumar gudanar da gasar kafin ranar dawowa.

Ya kuma gargadi kungiyoyin da su bada hadin kai wajen kawo musu sakamakon gwajin domin rashin yin hakan ka iya sanya a dakatar da kowace kungiya daga ci gaba da gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!