Labarai
Gwamna Abba Gida-gida ya tura wa majalisa ƙwarya-ƙwaryan kasafi na fiye da Biliyan 58
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar Kano, ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na fiye da Naira biliyan 58.
Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya bayyana hakan yayin da ya ke karanta wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar yayin zamanta na yau Litinin.
Ta cikin wasiƙar, gwamna Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci majalisar ta sahale masa kashe fiye da Naira biliyan 58 da miliyan 191 da dubu 535.
Haka kuma majalissar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta janyo ruwan sha daga madatsar ruwa ta garin Wudil zuwa Gano da Dawakiji da kuma Zogarawa da garin Gaya zuwa Jido.
Kiran ya biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu Shu’aibu Rabi’u, ya gabatar ya na mai bayyana cewa al’ummar yankin na fama da ƙamfar ruwan amfanin yau da kullum.
Shi ma mataimakin shugaban majalisar Muhammad Bello Ɓutu-ɓutu ya gabatar da ƙudurin neman gona titi a hanyar da ta tashi daga Mahuwa zuwa Janguza cikin gari ta dangana da garin Durum na ƙaramar hukumar Kabo.
You must be logged in to post a comment Login