Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya gabatar dakasafin baɗi na Tiriliyan 1 da Biliyan 107

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa Majalisar Dokoki daftarin kasafin kuɗin badi da ya kai kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 107.

 

Gwamnan ya ce kasafin, mai taken “Kasafin Ƙarfafa Nasarorin da aka Samu da Bunƙasa Ƙauyuka cikin Sauri,” zai mayar da hankali wajen kammala ayyukan raya ƙasa da a ke gudanarwa da kuma bunƙasa yankunan karkara.

 

Ta cikin Kasafin, gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan dari 693 da miliyan 47 kwatankwacin kashi 63 cikin 100, domin gudanar da ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware Naira biliyan dari 413 da miliyan 55, wato kashi 37 cikin 100, domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

 

Haka kuma, Gwamna Abba ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma sama da kashi 90 cikin 100 na manufofi da shirye-shiryen da ta tsara tun bayan hawanta mulki a shekarar 2023.

 

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da sanya ido kan yadda ake aiwatar da kasafin.

 

Kasafin na shekarar 2027 shi ne na huɗu kuma na ƙarshe a wa’adin mulkin farko na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!