Labarai
Sojoji sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a Niger

Dakarun Sojin kasar nan, sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mariga da ke Jihar Neja.
Rahotonni sun bayyana cerwa, jami’an sun samu wannan nasara ne a ranar Litinin din da ta gabata, bayan da su ka kai samame ƙauyukan Abaha da Sabon Wuri sakamakon bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’addar.
Rundunar sojin ta ce, dakarunta sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani daji, yayin da wasu kuma su ka samu raunukan harbin bindiga.
Jaridar Leadership, ta ruwaito cewa, dukkan mutane 21 da dakarun sojin su ka kubutar na cikin koshin lafiya, kuma ba bu wanda ya samu rauni.
You must be logged in to post a comment Login