Connect with us

Labarai

Kano: Babbar Kotu ta bayar da belin lauyan da ake zargi da yin damfara

Published

on

Babbar kotun jihar Kano ta bayar da belin Barrister Dalhatu Shehu Usman, wanda ake zarginsa aikata damfara da kuma ƙirƙirar takardun rasiti na bogi.

 

Mai shari’a Zuwaira Yusuf, ce ta bayar da belin nasa a yau Juma’a, bayan kotun ta yi watsi da ƙalubalen da lauyoyin wanda ake ƙara suka gabatar kan sahihancin izinin da babban lauyan gwamnatin jihar ya bayar domin gurfanar da shi.

 

Lauyan ma su ƙara, R.O. Zakariya, ya yi nasarar shawo kan kotun cewa rashin saka lambar shari’a a takardar izinin gurfanar da wanda ake zargin ba ya sa takardar ta zama ba ta da inganci, inda daga nan aka karanta wa wanda ake zargin tuhume-tuhume biyu, inda ya musanta aikata laifukan.

 

Jaridar SolaceBase, ta ruwaito cewa, mai gabatar da ƙara ya ƙi amincewa da bayar da belin, bisa hujjar cewa a baya wanda ake zargin ya gaza bayyana a gaban kotun, lamarin da ya sa aka bayar da sammacin kama shi, amma duk da haka, kotun ta amince da ba da belinsa tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Disamban  domin fara sauraron shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!