Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya raba takardun daukar aiki ga sabbin jami’an lafiya 2,037

Published

on

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi sabbin jami’an lafiya 2,037 da aka ɗauka aiki da su guji cin zarafin marasa lafiya ko karɓar na Goro kafin ba su kulawar da ta dace.

 

Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da rabon takardun ɗaukar aikin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce lokacin neman kuɗi kafin a kula da majiyyaci ya wuce, don haka ya buƙaci ma’aikatan da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, tausayi, ladabi da ƙwarewa.

 

Wasu daga cikin sabbin ma’aikatan sun bayyana farin cikinsu da samun aikin na dindindin, inda suka bayyana cewa hakan zai ba su damar samun kwanciyar hankali tare da ci gaba da yi wa al’ummar jihar hidima.

 

Sabbin ma’aikatan sun kuma yi alkawarin gudanar da aikinsu cikin gaskiya da kishin al’umma, tare da amfani da damar da aka ba su wajen inganta harkar kiwon lafiya.

 

Wadanda aka dauka aikin sun haɗa, da likitoci 250, ma’aikatan jinya 250, ungozoma 250, sai masu aikin ba da magani su 40, da manyan ma’aikatan lafiya na al’umma 150.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!