Connect with us

Labarai

Afirka ta Kudu ta gayyaci jakadan domin ya ta bahasi kan sukar gwamnatin kasar

Published

on

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta gayyaci jakadan Amurka Brent Bozell, domin ya ba da bahasi kan sukar gwamnatin kasar da ya yi a yayin wasu hirarraki da wasu kafafen yada labarai.

 

Wani jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ya ce wannan ne karo na uku da ake gayyatar mista Bozell, tun bayan nadin sa a matsayin jakada a 2025, saboda dabi’u da yake nunawa wadanda suka sabawa diflomasiyya. 

 

Rahotonni sun bayyana cewa, Shi dai Brent Bozell ya kasance mai ra’ayin mazan jiya, kuma Trump ya nada shi jakada ne a daidai lokacin da dangantaka ta fara yin tsami a tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka, musamman saboda batun shigar da karar Isra’ila a gaban kotun ICC da fadar mulki ta Pratoria ta yi kan zargin aikata kisan kare dangi a zirin Gaza.

 

Haka kuma shugaban Amurka Donald Trump na zargin mahukuntan Afirka ta Kudu da muzgunawa manoma farar fata da ake wa lakabi da ‘Afrikaners‘. 

 

Wannan dambarwa na zuwa ne makonni kadan bayan da Amurka ta sanar da daukar matakin takaita ba da biza ga wasu ‘yan Afirka ta Kudu a ranar 15 ga Satumba, ciki har da masu wanzar da dabi’ar wariyar launin fata.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!