Labarai
Mambobin ƙungiyar ƴan Gwangwan sun tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya

Ƙungiyar ƴan Gwangwan da masu sarrafa shara ta Najeriya NASWDEN, ta fara gudanar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu kamar yadda ya tai wa mambobinta umarnin fara wa daga yau 1 ga watan Oktoba.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Aminu Hassan Soja, Sarkin Ƙarafan ƙasar Hausa, ne ya bayyana hakan ya ganawarsa da manema labarai a Ƙofar shiga kamfanin sarrafa ƙarfafa na Youngxing da ke kan titin Western bypass da ke nan Kano a yau Alhamis.
Ya ce, ƙungiyar tasu ta fara wannan yajin aiki ne daga yau 1 zuwa 15 ga Oktoba, amma za a iya tsawaita shi idan ba a cimma yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanonin ƙarafan ba.
Alhaji Aminu Hassan Soja, bayyana maƙasudin wannan yajin aiki da cewa, ya samo asali ne sakamakon yadda baƙin haure masu kamfanoni ke zaftare mu su kuɗi tare da karya farashin ƙarfafa ba bisa ƙa’ida ba tare da yi wa ƙasar nan zagon ƙasa ta hanyar neman durƙusar da masu sana’ar ta Gwangwan.
Ƙungiyar ta kuma nuna zargi kamfanonin yin Rodi da almundahana ta hanyar rage kauri kayan da su ke sarrafawa ba tare da yin Ragin farashinsa daga yadda su ke sayarwa ba a baya duk kuwa da sun karya farashin yadda su ke sayen ƙarafuna daga ƴan Gwangwan.
Alhaji Aminu Hassan Soja, ya kuma ce, ƙungiyar tasu ta zauna da wakilan gwamnatin tarayya kan wannan batu na shirin tsundumarsu yajin aikin samar da ƙarafa ga kamfanoni, inda wakilan gwamnatin su ka sha alwashin shawo kan wannan matsala.
Latsa alamar Play da ke ƙasa don saurorin muryar sa.
You must be logged in to post a comment Login