Labarai
Gwamna Abba Kabir ya rantsar da sabbin masu ba shi shawara guda 21

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci rantsar da sabbin masu ba shi shawara na musamman guda 21, tare da sake tabbatar da wasu mutum shida a mukamansu.
Gwamnan, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci bikin rantsar da sabbin masu ba shi shawarar a yayin zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano karo na 41, wanda aka gudanar a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Gwamnan Abba ya bayyana cewa waɗanda aka ba wa amanar mukaman an dora musu babban nauyi na taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma manufofinta, tare da tabbatar da cewa ayyukan gwamnati sun kai ga al’ummar jihar.
Ya kuma buƙaci sabbin masu ba shi shawarar da waɗanda aka sake tabbatar da su da su kasance masu kishin aikin gwamnati, biyayya da kuma jajircewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma jaddada muhimmancin yin aiki tare tsakanin masu riƙe da mukaman gwamnati, domin tabbatar da kyakkyawan tsarin gudanar da ayyuka da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kano.
Wakilin mu na gidan Gwamnatin kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa Rantsar da sabbin masu ba gwamnan shawarar na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka wajen ƙarfafa tsarin gudanar da mulki da kuma tabbatar da samun ƙwararrun mutane da za su taimaka wajen ba da shawarwari kan harkokin gwamnati.
Bikin rantsarwar ya gudana ne yayin zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano karo na 41 a Abuja, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi gudanar da ayyukan gwamnatin jihar.
You must be logged in to post a comment Login