Labarai
Kotu ta soke takarar Pantami, ta umarci PDP ta sake zaben fidda gwani

Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Gombe ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaben fidda gwani domin fitar da dan takararta na gwamnan jihar.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin ne, bayan da Usman Aliyu Garry ya shigar da kara, yana kalubalantar zaman Prof. Isa Ali Pantami dan takarar PDP gwamnan jihar.
Garry ya kalubalanci Pantami ne bayan da PDP ta sanar da shi a matsayin dan takararta tilo a ranar 26 ga Yunin 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani da ya dace ba.
Pantami, wanda ya kasance dan takarar neman tikitin jam’iyyar APC, ya koma PDP ne bayan APC ta amince da Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na gwamna na masalaha.
Sai dai a hukuncin da ta yanke a yau Alhamis, kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaben fidda gwani, bisa ka’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zabe da suka dace.
You must be logged in to post a comment Login