Labarai
Kano ta zama jihar da ɗalibanta su ka fi cin Jarrabawar NECO ta bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandare ta Najeriya NECO, ta bayyana jihar Kano a matsayin wadda dalibanta sukafi cin jarrabawar ta bana.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Dantani Wushishi ya fitar a shafinta hukumar na Internet a yau Laraba 24 ga watan Satumbar 2026.
Sanarwar ta ce Dalibai dubu dari da ashirin da biyu da dari tara da uku ne suka samu Credit 5 da Ingilishi da kuma Lissafi.
Jihar Lagos ce ta kasance ta biyu daga cikin jihohin da suka samu sakamako mai kyau a jarrabawar inda dalibai dubu sabain da biyu da dari hudu da arbain da shida suka samu Ingilishi da Lissafi.
You must be logged in to post a comment Login