Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya yi Alla-wadai da hare-haren da ƴan bindiga su ka kai sassan Kano

Published

on

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Alla-wadai da hare-haren ƴan bindiga da aka kai a wasu sassan jihar, inda ya ce, gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin ƙara tsaurara tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda ya ce gwamnan ya ce hare-haren sun shafi Chiromawa da ke ƙaramar hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji da wasu yankuna da ke kewaye da Gwarzo.

 

Haka kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu, yana mai bayyana hare-haren a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba inda aka umarci hukumomin da abin ya shafa da su ƙara kaimi wajen tattara bayanan sirri, sa ido da kuma gaggauta kai ɗauki a yankunan da abin ya shafa.

 

Gwamnan ya buƙaci al’umma su kwantar da hankula tare da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai, musamman ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a hare-haren.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!