Labarai
Atiku ya soki tsarin rancen kudin karatu na NELFUND

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki tsarin rancen karatu na NELFUND, ya na mai cewa rance ba tallafin karatu ba ne, bashi ne da ɗalibi zai biya.
Atiku, ta bakin mai magana da yawunsa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027, zai rage kuɗaɗen ilimi tare da yafe basussukan ɗaliban da suka cancanta bayan gudanar da cikakken nazari kan tsarin.
Atiku ya kuma kalubalanci gwamnatin Tinubu da ta fitar da bayanan lissafin da ke nuna yadda shirin rage farashin man fetur da yake gabatarwa zai shafi NELFUND, albashin ma’aikata ko mafi ƙarancin albashi.
You must be logged in to post a comment Login