Connect with us

Labarai

Ministan tsaro ya gargadi Gwamnoni kan rabon babura

Published

on

Ministan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa, ya gargadi gwamnoni da ‘yan majalisu kan rabon babura a matsayin tallafi, wanda yace wasu daga cikinsu na iya komawa hannun ‘yan ta’adda.

Janar Musa ya ce baburan na bai wa ‘yan ta’adda damar yin zirga-zirga cikin sauri da tserewa jami’an tsaro, musamman a yankunan da ke da dazuzzuka da hanyoyin karkara.

Ya kuma ce hukumomin tsaro sun gano wasu kasuwanni da tashoshin motoci ba bisa ka’ida ba, wadanda ake amfani da su wajen safarar makamai da alburusai zuwa wuraren da ‘yan ta’adda ke aiki.

Ministan ya yi kira da a ƙara bai wa ƙananan hukumomi damar taka rawa wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da gudanar da tarukan tsaro akai-akai da kuma sa ido kan kasuwanni da tashoshin motoci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!