Labarai
Majalisar Dattawa ta amince da dokar kafa ƴan sandan jihohi

Majalisar Dattawa ta amince da kudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi, lamarin da ya sake ba da karfi ga muhawarar da aka dade ana yi kan bukatar samar da rundunar ‘yan sanda a matakin jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Majalisar Wakilai ta amince da kudirin mai taken gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 domin kafa ‘yan sandan jihohi da sauran batutuwa masu alaka da hakan.
Shugaba Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa wasika a ranar Talata inda ya bukaci a gaggauta duba kudirin,Hakan ya sa shugaban masu rinjaye a majalisar, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da shi domin karatu na farko, na biyu da na uku.
Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce idan aka kammala amincewa da kudirin za a tura shi zuwa majalisun dokokin jihohi domin ci gaba da tantance shi.
Yayin da yake jagorantar muhawarar, Bamidele ya bayyana cewa an shafe sama da shekaru biyu ana tattaunawa kan kudirin tare da karbar ra’ayoyin masu ruwa da tsaki daga sassan kasar nan.
Haka kuma kudirin ya tanadi matakan kariya daga amfani da rundunar wajen siyasa, da kafa kwamitocin kula da ‘yan sandan jihohi masu zaman kansu, tare da tabbatar da daidaitattun ka’idojin aikin ‘yan sanda a fadin kasa.
You must be logged in to post a comment Login