Labarai
Gwamna Abba ya aika wa majalisa kudurori 3 da ya ke so su za ma doka

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasu kudurori uku daga gwamnatin jihar, da nufin inganta harkokin kiwon lafiya da kuma yadda ake tafiyar da ayyukan lafiya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tura kudurorin ga Majalisar domin duba su da kuma ɗaukar matakin da ya dace.
Kudurorin sun haɗa da gyaran dokar hukumar kula da magunguna da kayayyakin lafiya da dokar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko da kuma kafa kwalejojin lafiya uku masu cin gashin kansu.
A wata wasiƙa da Gwamnan ya aika wa shugaban Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya buƙaci ’yan majalisar su duba kudurorin tare da yin nazari akan su yadda ya dace.
Kwamitin Majalisar mai kula da ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ya tabbatar da Salihi Adamu a matsayin Sakataren ƙaramar hukumar Takai.
You must be logged in to post a comment Login