Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci a dauki matakin gaggawa kan barkewar Diphtheria

Published

on

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa kan barkewar cutar Diphtheria cutar mashako, wadda rahotanni suka ce ta hallaka fiye da yara 50 a karamar hukumar Rano.

 

Dan majalisar mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad, ya ce cutar ta fi yin kamari a yankunan Rurum da Sabuwar Ƙaura, inda ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Lafiya su kara tura magunguna da ma’aikatan lafiya yankunan.

 

Da suke goyon bayan ƙudurin, wasu daga cikin ‘yan majalisar sun ce cutar ta bazu zuwa karamar hukumar Kiru, inda ta shafi Kwanar Dangora da Dangora da kuma Yelwa.

 

Majalisar ta amince da kudirin tare da umartar kwamitinta mai kula da harkokin lafiya da ya tattauna da ma’aikatar lafiya kan aiwatar da dokar kare lafiyar jama’a da kuma samar da agajin gaggawa ga al’ummomin da abun ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!