Labarai
Gwamnatin Kaduna ta kafa kwamitin da zai tattaunawa da ƙungiyar ASUU

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin mutane tara domin tattaunawa da ƙungiyar malam jami’o’i ASUU reshen Jami’ar Jihar da sauran ƙungiyoyin ma’aikata kan buƙatunsu da ba a warware ba.
Haka kuma, gwamnatin ta amince da biyan malaman jami’ar Naira miliyan 300 a matsayin kuɗaɗen Alawus.
Hakan na cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar ta Kaduna, Dakta Abdulkadir Meyere, ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce, an kafa kwamitin ne domin duba buƙatun kungiyoyin wadanda suka hada da ASUU da SSANU da NASU da kuma NAAT, tare da kwatanta yanayin aiki a Jami’ar ta Kaduna, da sauran jami’o’in wasu jihohin.
Abdulkadir Meyere, ya ce, gwamnatin, ta kuma kafa tsarin ware Naira miliyan 50 duk wata domin biyan basussukan ma’aikata, tare da kashe sama da Naira miliyan 300 wajen tantance shirye-shiryen karatu da sauran ayyukan inganta jami’ar.
ya kuma bayyana cewa, Kwamitin zai kammala aikinsa ne cikin makonni huɗu,
You must be logged in to post a comment Login