Labarai
Gwamna Abba ya ba da filaye 1,540 da miliyan 100 ga shugabannin ƙungiyar yan APC

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya raba kyautar filaye 1,540 da naira miliyan 100 ga shugabannin ƙungiyar masu goyon bayan APC a matakin rumfunan zaɓe wato ‘yan akwati, da nufin ƙarfafa musu gwiwar tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027 mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana bada kyautar ne lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ƙungiyar ta ‘yan akwati waɗanda zasu yiwa jam’iyyar APC aiki a mazaɓun a lokacin zaɓe.
Gwamnan ya ce yunƙurin ƙarfafa jam’iyya tun daga tushe zai taimaka wajen tabbatar da samun nasarar Shugaba Bola Tinubu da kuma sauran ‘yan takarar APC a dukkan zaɓukan da za’a gudanar
Ya kara da cewar, sake zaɓen Shugaba Tinubu zai bada damar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa, wanda hakan ce ta sanya gwamnati baiwa ƙungiyar kyautar filaye da tallafin naira miliyan ɗari domin gudanar da ayyukanta.
Da ya ke jawabi yayin taron, mai bai wa gwamna Abba shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Mustapha Hamza Buhari Ba-kwana, ya ce, tallafin shi ne matakin farko na shirin tattara magoya bayan APC gabanin zaɓen shekarar 2027 da ke tafe, inda ya ce ‘yan Akwatin kaɗai na da ƙarfin tara wa shugaba Tinubu ƙuri’u sama da miliyan ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login