Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta gyara hanyoyin samar da ruwa a Warawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta fara tura ruwa zuwa ƙaramar hukumar Warawa bayan shafe sama da shekaru biyar ba tare da samun ruwa ta manyan bututun rarraba ruwa ba.

Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Sauyin Yanayi ta jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana hakan yayin duba ayyukan cibiyoyin tace ruwa na Wudil da Joda.

Ya ce an fara gwajin tura ruwa ne domin tantance matsin ruwa da kuma gano wuraren da bututun ke zubar ruwa, yana mai cewa idan an kammala gwajin, ruwa zai rika isa har zuwa Rijiyar Gwan-gwan. Ya kuma ce za a fara irin wannan gwaji a hanyoyin rarraba ruwa na Gaya da Dawakin Kudu nan ba da jimawa ba.

Ya ce cibiyar tace ruwa ta Wudil ta samu ci gaba bayan an haɗa ta da wutar lantarki ta Band A, lamarin da ya ƙara sa’o’in samun wuta daga kusan awa ɗaya zuwa tsakanin awa 18 zuwa 22 a rana, abin da zai ba ta damar samar da ruwa yadda ya kamata ga al’ummomin Wudil. Haka kuma ya ce cibiyar tace ruwa ta Joda ta koma samar da ruwa ga wasu al’ummomin ƙaramar hukumar Gabasawa tare da amfani da rijiyoyi bakwai, yayin da ake sa ran ƙara wasu biyar domin ta kai cikakken ƙarfin aikinta.

Dakta Dahiru Hashim ya ce gwamnati na ci gaba da gyaran cibiyoyin ruwa da sauran muhimman gine-gine domin tabbatar da dorewar ayyukan samar da ruwa. Ya kuma yabawa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa fannin samar da ruwa domin tabbatar da isar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummomin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!