Labarai
Kano: Hukumar Hisbah ta haramta yin sana’ar tura fina-finai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da haramta yin sana’ar tura fina-finai watau Downloading a faɗin jihar, bisa zargin wasu masu sana’ar na yin amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar na Jihar Kano, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radiyo.
Dakta Mujahiddin, ya ce, daukar matakin ya biyo bayan korafe-korafen da hukumar ta samu daga alummar jihar, kan yadda wasu masu sana’ar ke amfani da ita wajen yaɗa bidiyoyin batsa, lamarin da ya ce na lalata tarbiyyar yara da matasa.
You must be logged in to post a comment Login