Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kwamitin bincike kan zargin karkatar da abincin yara

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani kwamiti domin gudanar da bincike kan zargin karkatarwa da sace da kuma sayar da kayan abincin yara, wato Tamowa a fadin Jihar.

Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ƙaddamar da kwamitin.

A cewar kwamishinan an kafa kwamitin ne domin gano gaskiyar abin da ya faru dangane da zargin karkatar da kayayyakin da aka tanada domin ceton rayukan yara masu fama da cutar tamowa, tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Haka kuma, kwamitin zai tantance adadi da kuma kimar kayayyakin da suka bace, sannan ya bayar da shawarwari kan matakan hukunci da gyaran da ya dace, tare da gabatar da rahotonsa cikin kwanaki goma sha hudu daga ranar kaddamar da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira miliyan dari biyar wajen sayo wadannan kayayyaki domin kula da yara masu fama da cutar Tamowa.

Babban sakataren na ma’aikatar Aminu Bashir, ne zai jagoranci kwamitin, wanda ya kunshi mambobi goma sha takwas daga hukumomi da bangarori daban-daban da suka haɗa da jami’an tsaro, wakilan masarauta da masu unguwanni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!