Coronavirus
Gwamna Badaru ya dinkawa Almajirai kayan sallah
Gwamnatin jihar Jigawa ta dinkawa Almajirai ‘yan asalin jihar da gwamnatoci wasu jihohi suka mayar mata dasu kayan sallah.
Kwamishinan lafiya na jihar Jigawa Dr. Abba Zakari ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu Aminu Umar Shuwajo.
Dr. Abba ya ce sun yiwa almajiran gwajin cutar Corona wanda sakamakonsa ya nuna wasu na dauke da cutar, wadanda yanzu haka na cigaba da samun kulawa a cibiyar killace masu cutar Corona dake Jigawa.
Karin labarai:
Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa
Mutum na farko da ya kamu da Corona ya isa jihar Jigawa
Har ila yau kwamishinan ya ce yanzu haka tuni suka fara mayar da sauran almajiran da aka samu basu da cutar Covid-19 zuwa hannun iyayensu, bayan sun dinka musu kayan sallah da kuma tukwicin naira dubu goma-goma kowannensu.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da gwamnatocin jihohi ke cigaba da mayar da almajiran dake bara a jihohinsu zuwa garuruwansu na asali.
Wakilin Freedom Radio a Jigawa Aminu Umar Shuwajo ya rawaito mana cewa gwamnan jihar ta Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yayi alkawarin cewa ba zai mayar da almajiran da ba ‘yan asalin jihar sa ba, dake zaune a jihar har sai bayan wucewar annobar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login