Labarai
Gwamna Ganduje na jagorantar kwamitin binciken rikicin siyasar jihar Edo
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jagoranta kwamitin na mutane biyar karkashin jami’yyar APC dangane da rikicin da ke afkuwa a jam’iyyar ta APC a jihar Edo.
Sakataren jamiyyar ta kasa Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana haka a yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida.
idan za’a iya tunawa dai jamiyyar APC ta kasa ta kafa kwamitin da zai binciki matsalar da ke faruwa a jam’iyyar reshen jihar Edo wanda gwamna Abdullahi Ganduje ke jagoranta.
Mambobin da ke cikin kwamitin dai akwai gwamnan jihar Katsina , Aminu Masari da tsohon gwamna Oyo Abiola Ajimobi da tsohon gwamnan jihar Borno sannan sanata Kashim Shettima da Ahmad Wadada wanda shine sakataren kwamitin.
Tuni dai ‘yan jam’iyyar suka fara damuwa kan jan kafa da kwamitin yake wajen bayyana sakamakon rahoton sa.
Ya kara da cewa tuni aka basu ka’idojin da zasu yi amfani da shi wajen gudanar da binciki , a don haka ne aka zabi wadanda ke cikin kwamitin don samun sakamakon da ya dace.
Yau Ganduje da Abba kowa zai san matasayin sa-Kotun daukaka kara
Ganduje ya rantsar da kwamishinoni ranar tantancewa
Ganduje ya sabunta yarjejeniyar tallafin karatun Digiri na biyu da kasar Faransa
Sakataren jamiyyar ya ce ba zasu iya tantancewa ko kwamitin ya fara aiki ba tare da sun bayyana sakamakon ba.
Akwai dai rashin jituwa da ke faruwa tsakanin gwamna Godwin Obaseki da shugaban jamiyyar Adams Oshiomole, a halin yanzu
Kwanankin baya ne dai shugaban jamiyyar ta APC ya zargin gwamna Edo da aiko da ‘yan bangar siyasa a filin da ake taron yaye dalibai dake Edo domin su tozarta shi.