Labarai
Gwamna Ganduje ya bukaci mutane su zauna a muhallansu yayin Kidaya
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar jihar da su zauna a muhallanu lokacin gudanar da kidayar da za a gudanar a watan mayu mai kamawa domin tabbatar da cewa an kidaya su.
Gwamna Ganduje, ya bukaci hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin wayar da Kan jama’a game da kidayar mutane da gidaje a fadin Nijeriya yayin dasuka kai ziyara fadar gwamnatin Kano.
Haka kuma ce sai an san yawan al’umma ne sannan za a san yadda za a inganta rayuwar su har ma da ware kasonsu a rabon tattalin arziki kasa.
A nasa jawabin shugaban kwamitin wayar da kan jama’a game da kidaya Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad, wanda Babban Daraktan hukumar wayar da kai ta Nijeriya NOA Garba Abari, ya wakilta ya ce, akwai dokokin da ya kamata mutane su sani game da aikin kidayar.
Garba Abari, ya kuma bukaci mutane su kauce wa yada labaran karya game da kidayar da za a gudanar.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login