Labarai
Gwamna Mai Mala na Yobe ya jagoranci buɗe gidan ruwa a Sokoto

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranci buɗe sabon gidan ruwan da Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya samar a garin Dambuwa da ke cikin jihar Sokoto.
Ginin gidan ruwan ya zo ne a dai-dai lokacin da al’ummar jihar Sokoto ke fama da matsanancin karancin ruwan sha, wanda ya jawo koke da damuwa daga jama’a.
Taron buɗe gidan ya samu halartar muhimman mutane a ciki da wajen jihar, ciki har da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.
You must be logged in to post a comment Login