Addini
Gwamna Masari ya soki Sheikh Gumi kan batun sulhu da ‘yan bindiga
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya caccaki fitaccen malamin addinin islaman nan da ke Kaduna Sheikh Ahmed Gumi sakamakon neman sulhu da ya ke kokarin ganin anyi da ‘yan bindiga da ke aikata ta’asa a yankin arewa.
Gwamnan na Katsina ya ce shi kam sam bai gamsu da salon da Shehin malamin ke bi ba wajen neman sasanci da ‘yan bindigar.
A tattaunawa ta cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels (Politics Today) gwamnan na Katsina ya soki salon Sheikh Gumi, har ma ya gayace shi da su fuskanci juna su yi muhawara kan wannan batu.
‘‘Me Sheikh Gumi ya sani game da matakin da muka dauka a Kaduna? Na kalubalance Sheikh Gumi da ya zo ya gayamana ko me muka yi a Kaduna’’
‘‘Maganganun da ‘yan bindiga suke fada masa a yanzu, irinsa ne dai suka rika fada a shekarar dubu biyu da goma sha biyar, irinsa suka saka fada a 2019’’
Wai ma nace, me Sheikh Ahmed Gumi ya sani game da dazuka? So ya ke yi a karfafa gwiwa ga ‘yan ina da kisa ko me ya ke nufi’’?
‘‘Sam ko kadan bana goyon bayan salon Sheikh Gumi wajen kawo karshen ta’addancin ‘yan bindiga, saboda bai bi hanyoyin da suka kamata ba wajen kawo karshen matsalar’’.
‘‘Na yi tsammanin cewa, zai yi musu wa’azi ne kan illar kashe mutum ba da hakkinsa ba, da kuma girmar laifin da ke tattare da sace mutane ana garkuwa da su a mahangar addinin Islama’’.
Abin da na yi zaton duk malamin addini zai yi kenan idan zai gana gaba da gaba da ‘yan ta’adda’’ a cewar gwamna Masari.
You must be logged in to post a comment Login