Labarai
Gwamna Mutfwang ya sanya dokar takaita zirga-zirga

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya saka sababbin matakan kariya na takaita zirga-zirga a wasu sassan jihar, biyo bayan kashe kashen al’umma da aka yi a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, inda ya bayyana harin a matsayin kisan gilla da ake kai wa jihar da gangan, yana mai cewa jihar ta Filato ba za ta rushe ba.
Daga cikin matakan da aka dauka akwai haramta kiwon dabbobi da daddare a fadin jihar baki daya, kana gwamnati ta hana jigilar shanu bayan karfe 7:00 na yamma, sannan an takaita zirga-zirgar babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana alhinin sa kan harin da aka kai kauyen Zikwe da ke karamar hukumar Bassa a daren Lahadi, 13 ga Afrilu, wanda harin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin rasa sama da rayuka 50 a wani mummunan hari da aka kai garin Bokkos lamarin da ya jefa jihar cikin tashin hankali.
You must be logged in to post a comment Login