Labarai
Flying Eagles za ta buga wasan sada zumunta da Kogi United

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ‘yan kasa da shekaru 20 Playing Eagles, za ta buga wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta Kogi United.
Ta cikin wata sanarwa da mai horas da kungiyar Kogi United, Tijani Ibrahim, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, kungiyar ta bayyana cewa, za a buga wasan ne a filin wasa na Mashood Abiola da ke birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis 17 ga Afrilun bana da misalin karfe 4:00 na yamma.
You must be logged in to post a comment Login