Labarai
Yan Sanda sun daƙile harin da ’yan bindiga suka kai ofishin su a Benue

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan kwantar da tarzoma watau Mobile Police, sun daƙile harin da ’yan bindiga suka kai kan ofishin su da ke Jootar a jihar Benue.
Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar da ke hedikwatar ta a Abuja, CSP Ani Iniedu, ya fitar a ranar Litinin 10 ga Agusta, 2026.
Ya ce, Jami’an ’yan sandan sun mayar da martani cikin gaggawa da ta hanyar bude wuta, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigan tserewa.
Sanarwar ta ce, Binciken farko ya nuna cewa maharan sun yi niyyar kai farmaki chaji ofishin, kafin su kai hari kan wasu mutane da ke yankin.
Ya ce, wani Mlanga Gbange, ya samu rauni a ƙafa sakamakon harsashin da ya kuskure, inda aka kai shi Asibitin St. Anthony da ke Zaki Biam domin samun magani.
Rundunar ta ce, babu wani jami’inta da ya jikkata yayin artabun, inda ta ce ta na ci gaba da bincike kan lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na SCID da ke Makurdi.
You must be logged in to post a comment Login