Labarai
Gwamnan Bauchi ya sauke Kwamishinar harkokin mata da ƙananan yara

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da sauke Kwamishinar harkokin mata da ci gaban ƙananan yara ta jihar Zainab Baban-Takko.
Mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Mukhtar Gidado, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Litinin.
A cewarsa daukar matakin ya biyo bayan wani dan karamin sauyi da gwamnan jihar Bala Muhammad Abdulkadir ya yi kan majalisar zartaswar jihar.
You must be logged in to post a comment Login