Kiwon Lafiya
Gwamnan Kano ya bukaci malaman addinai su yi amfani da masallatai da coci-coci wajen kiran mabiya su rungumi zaman lafiya
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci malaman addinai a fadin jihar da su yi amfani da masallatan su da coci-coci wajen kiran mabiyan su da su rungumi zaman lafiya, inda ya ce gwamti zata ci gaba da gudanar da taruka daban daban ga mabiya addinai domin fadakar da su muhimmancin zaman lafiya.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin taron wuni daya da Yamai da hankali kan karfafa alaka da fahimtar juna tsakanin addinai domin ciyar da jihar Kano gaba da ya gudana yau a fadar gwamnatin jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnatin sa ta maida hankali ainun wajen tabbatar da zaman kafiya a tsakanin mabiya ddinani a fadin jihar nan.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar kiristoci na jihar Kano Reverend Adeyemu Samuel ya jaddada cewar mabiya addinin kirastanci a jihar nan za su ci gaba da yin duk abin da ya da ce domin wanzar da zaman lafiya a jihar nan.
taron ya samu halartar manyan malamai da ga dukkan bangarorin addinai da suka hadar da Malam Tijjani zangon Barebari da kuma chief Boniface Ibekwe da dai sauransu.