Labarai
Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudi na 2026 da ya haura Tiriliyan Daya

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai kimanin tiriliyan daya da Bilyan 368 a gaban majalisar dokokin jihar Kano, wanda aka yi wa laƙabi da “Kasafin Gine-gine, da Ci gaba Mai Dorewa da Haɗin Kai”.
Kasafin kuɗin na bana ya fi karkata ne ga manyan ayyukan raya ƙasa, inda kaso 68 na kuɗin suka tafi ga ayyukan ci gaba, yayin da 32 suka tafi ga ayyukan bukatun yau da kullum.
Bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka da ya kai Biliyan 405, domin gina makarantu da gyare-gyare da ƙarin malamai sai ci gaba da bayar da ilimi kyauta da kuma bayar da tallafin jami’a.
Yayin da Kiwon lafiya ya samu Biliyan 212 don sabunta asibitoci da samar da kayayyakin aikin jinya da ƙarfafa inshorar lafiya.
You must be logged in to post a comment Login