Labarai
Gwamnan Kano ya sake sabbin naɗe-naɗe guda 9
A ƙoƙarin sa na ciyar da jihar kano gaba Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake naɗa manya masu bashi shawara na musamman domin tallafa mai a wasu daga cikin ma’aikatun gwamnati.
Wannan na ƙunshe ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau talata.
Wa’inda aka naɗa su ne kamar haka.
1. Farfesa Ibrahim Magaji Barde, a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR).
2. Dr. Abdulhamid Danladi, mai bashi shawara na musamman kan harkokin kasashen waje II
3. Engr. Bello Muhammad Kiru, mai bashi shawara na musamman kan albarkatun ruwa.
4. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) ya sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.
5. Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, a ma.aikatar Ruwa da Gine-gine (WRECA).
6.Haka kuma Baba Abubakar Umar ya samu sauyi daga mai bawa gwamna Kano shawara na musamman ga harkokin makarantu masu zaman kansu zuwa maaikatar dake kula da ma.aikatan wucin gadi
7. Hon. Nasir Mansur Muhammad an nada shi shugaban hukumar, Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs).
8. Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin shugaban Hukumar kula da Albarkatun Noma Raya Karkara ta Kano (KNARDA).
9. Engr. Mukhtar Yusuf, Mataimakin shugaban hukumar kula da Albakatun Ruwa da Gine Gine (WRECA).
Kuma gwamnan ya umarci naɗin ya fara aiki nan take domin ciyar da kano gaba.
You must be logged in to post a comment Login