Labarai
Gwamnan Zamfara ya gabatar da kasafin kudin badi

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin jihar.
Kasafin da gwamnan ya gabatar dai ya haura kimanin Naira biliyan 861.
Da ya ke gabatar da daftarin kasafin, gwamnan Dauda Lawal ya ce, kaso 83 cikin 100 na kasafin zai tafi a bangaren manyan ayyuka, inda aka ware Naira biliyan 715 domin gudanar da su.
Gwamna Dauda Lawal Dare, ya kara da cewa an kuma ware wa bangaren ayyukan yau da kullum kimanin Naira biliyan 147.2, wanda ya kama kashi 17 cikin 100 na kasafin kuɗin.
You must be logged in to post a comment Login