Labarai
Gwamnati bata zurfafa bincike kan farashin fetur na Najeriya na da araha – NLC
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Ayuba Wabba ya ce da alama gwamnatin tarayya bata zurfafa bincike ba, kan ikirarin ta na cewa farashin man fetur a kasar nan na cikin mafi Arha a nahiyar Africa.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar litinin din da ta gabata ne ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji lai Muhammad ya yi ikirarin cewa duk da Karin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, amma farashin man a Najeriya na cikin mafi arha a kasashen Nahiyar Africa.
Da ya ke zantawa da Manema Labarai Ayuba Wabba ya ce a halin da ake ciki kamata ya yi gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan yadda darajar Naira ta karye ga shi kuma Naira dubu 33 ne kadai mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan.
Wabba ya ce yin wancan ikirarin na gwamnatin tarayya abin takaici ne, kasancewar ba wai iya farashin man fetur aka kara a kasar nan ba, wanda hakan kuma ke tayar da hankalin al’ummar kasar nan.
Ya ce Karin farashin man fetur da na wutar lantarki a dai-dai lokacin da kayan masarufi ke kara tsada abu ne mai matukar hadari don kuwa zai iya tunzura al’ummar kasar nan su dauki matakin da bai da ce ba.
You must be logged in to post a comment Login