Labarai
Gwamnati ta fara daukar ma’aikatan wucin gadi a Kaduna
A jihar Kaduna, an fara daukar matasa su dubu ashirin da uku ayyuka na wucin gadi, ta cikin shirin nan na gwamnatin tarayya na daukar mutane dubu daidai a kowace karamar hukumar.
An dai fara ne a yau asabar, wanda ya gudana a Fatika da ke yankin karamar hukumar Giwa a jihar ta Kaduna, karkashin bin dokokin kariya daga kamuwa daga cutar corona.
Da take jawabi yayin bikin fara daukar ma’aikatan da ke karkashin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, shugabar kwamitin zabar ma’aikatan kuma kwamishiniyar ayyukan walwala da ci gaban al’umma na jihar, Hajiya Hafsat Baba, ta ce, shirin na daukar ma’aikatan da gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar yi guda dubu 774, 000 a jihohi 36 kasar zai taimaka gaya wajen rage zaman banza tsakanin matasa.
Hajiya Hafsat Baba ta kuma ce, za su yi iya kokarinsu wajen ganin matasan jihar sun amfana da shirin yadda ya kamata don magance matsalolin rashin aikin yi a tsakani matasa.
Ta kara da cewa, ‘yan siyasa a jihar Kaduna za su samu kaso 13 na gurbin daukar ma’aikatan, yayin da kaso 87 za a duba matasan da suka cancanta karkashin kwamitin don basu damar morar shirin.
You must be logged in to post a comment Login