Labarai
Gwamnati ta sake nazari kan dokar kalaman batanci
A dai kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta sake yin nazari kan dokar da ta kafa hukumar kula da kafafan yada labarai ta kasa akan kudin dake cin tara na kalaman batanci daga Naira dubu dari biyar zuwa miliyan biyar.
Da yake maida martini kan kalaman da ake yadawa kan yawan kudin da aka kara a wata kafar Talabijin, ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce an sake nazarin sabon kudin tarar ne don ya zama izina ga kafafan yada labarai dake yada kalaman batanci.
Da yake buga misali da kisan kiyashin da aka yi a kasashen Ruwanda da Bosnia Herzegovina da kuma Combodia Lai Muhammed ya ce kalaman batanci ne ya rura wutar rikicin, a don haka ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta managance wannan matsalar.
You must be logged in to post a comment Login