Kiwon Lafiya
Gwamnatin Benue da Taraba sun yi afuwa da tubabbun yan ta’ada da ke ta’addanci a jihohin biyu
Gwamnatin jihar Benue da ta jihar Taraba sun amince su yi afuwa ga tubabbun yan ta’dda da ke ayyukan su na ta’addanci akan iyakokin jihohin biyu, in dasuka ce za su hada karfi da su wajen karfafa al’amuran tsaro.
Rahotanni sun yi nuni da cewa damar yin afuwa ga yan ta’addan wani bangare ne, na matakin da aka dauka bayan wani taron karfafa tsaro a tsakanin jihohin biyu da ya gudana a jami’ar Wukari dake jihar Taraba.
Gwamna Dariyos Ishaku na jihar Taraba wanda ya karanta jawabin bayan taro jim kadan bayan da karkare ziyarar kan iyakokin jihar, ya ce shirin afuwa ga tsagerun ya fara aiki ne nan take, zai kuma kare a karshen watan Janairun sabuwar shekara.
A yayin taron gwamnonin jihohin biyu sun yi alawadai da yawaitar satar mutane da ake samu a jihohin biyu, da kuma fashi da makami da kuma tare hanya domin sata da matasa ke yi a jihohin.
Haka kuma gwamnonin jihohin biyu sun jaddada muhimmancin da ke akwai wajen samarwa matasa ayyukan yi, a cewar su rashin aikin yi ne ke jefa matasan cikin halin da suka tsinci kan su a ciki.